’Yan sanda sun kama wanda ya yi garkuwa da jikansa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama mutum uku da ake zargi da laifin yin garkuwa da wani yaro a garin Tudun Wada da ke jihar ciki har da wani kakan yaron. Da yake nuna wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandaa da ke Kano, Kakakin rundunar ASP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa tun […]

’Yan sanda sun kama wanda ya yi garkuwa da jikansa
’Yan sanda sun kama wanda ya yi garkuwa da jikansa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama mutum uku da ake zargi da laifin yin garkuwa da wani yaro a garin Tudun Wada da ke jihar ciki har da wani kakan yaron.

Da yake nuna wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandaa da ke Kano, Kakakin rundunar ASP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa tun a ranar Talatar makon jiya ne wani mutum da ake kira Bello Wada da Aliyu Tasi’u da wata Fauziyya Bala da kuma wani Hamisu SNU wanda ake nemansa suka hada kai suka yi sace wani yaro dan kimanin shekara hudu mai suna Umar Aminu Ibrahim a gidan mahaifinsa da ke garin
Tudun Wada.
A cewar Majiya wanda ake zargi na biyu wato Aliyu Tasi’u kani ne ga kakar yaron da aka sacen. Ya ce Aliyu Tasi’u ya shiga gidan kakar yaron ne, ya dauke mata hankali da hira inda shi kuma Bello Wada ya yi amfani da wannan damar ya sace yaron tare da damka shi ga hannun Fauziyya Bala a unguwar Tarauni a birnin Kano.
“Daga nan ne kuma suka kira kakar yaron a wani sabon layin wayarta da mutane kadan ne suka san lambar, inda suka nemi a biya Naira miliyan uku a matsayin fansar yaron ko kuma su kashe shi. Daga nan ne yan uwan yaron ciki har da wadanda ake zargi suka je ofishin ’yan sanda da ke garin Tudun Wada suka sanar da jami’anmu,” inji Majiya.
Majiya ya kara da cewa “A take jami’anmu suka fara bincike inda kuma suka yi nasarar kame wadanda ake zargin tare da tserar da yaron lami lafiya, ba tare da biyan kudin fansar ba.”
Ya ce a yanzu haka sun mika batun ga ofishin da ke kula da manyan laifuffuka na jihar don yin cikakken bincike tare da gurafanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.