‘Yan sanda sun kama wanda ya yi yunkurin kisan kai

Hukumar ‘yan sanda sun tsare wani matashi mai suna Idris Abubakar  da ke zaune a Unguwar Maganda a Karamar Hukumar  Doguwa akan zarginsa da yunkurin kisan kai. A wata sanarwa da kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar Kano SP Magaji Musa Majiya ya sanar na cewa, an tsare wanda ake zargin ne a ranar 11 ga […]

‘Yan sanda sun kama wanda ya yi yunkurin kisan kai

Hukumar ‘yan sanda sun tsare wani matashi mai suna Idris Abubakar  da ke zaune a Unguwar Maganda a Karamar Hukumar  Doguwa akan zarginsa da yunkurin kisan kai.

A wata sanarwa da kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar Kano SP Magaji Musa Majiya ya sanar na cewa, an tsare wanda ake zargin ne a ranar 11 ga watan Nuwamba 2018 a wata mota kirar taxi mai dauke da makaimai da bindiga kirar gida, a hanyarsa na zuwa rukunin gidaje da ke Rijiyar Lemo da nufin kashe abokin kasuwancinsa wanda yake binsa kudi Naira dubu 480.