’Yan sanda sun kama wanda zai sayar da dansa
Wani matashi, dan shekara sama da 30 ya shiga hannun ’yan sanda, a lokacin da ya je unguwar Layin Bagobiri a Kalaba yana neman wanda zai sayi dansa.Majiyar Aminiya ta samu labarin yadda mutumin ya je unguwar Hausawa a Kalaba, inda aka fi sani da layin Bagobiri tallar wani yaro karami,wanda kuma akekyautata zaton dansa […]
Wani matashi, dan shekara sama da 30 ya shiga hannun ’yan sanda, a lokacin da ya je unguwar Layin Bagobiri a Kalaba yana neman wanda zai sayi dansa.
Majiyar Aminiya ta samu labarin yadda mutumin ya je unguwar Hausawa a Kalaba, inda aka fi sani da layin Bagobiri tallar wani yaro karami,wanda kuma akekyautata zaton dansa ne zai sayar .
Da wakilinmu ta tuntubi ofishin gunduma na ’yan sandan Atakpa a Kalaba, sun tabbatar da aukuw alamarin, har ma suka nuna mai laifin da cewa,” ga shi nan a hannu.”
A bayanin da Aminiya ta samu shi ne, wannan mutum ya zo ya “samu wasu Hausawa ya ce musu yana da mutum na sayarwa, yaro karami.
“Cikin hikima suka ce masa ya je ya kawo, kafin ya dawo, su kuma suka sanar da Sarkin Hausawa Alhaji Salisu Abba Lawal, inda shi kuma ya sanar da ofishin mu. Su kuma ba su yi kasa a gwiwa ba, suka kiramu nan take muka tura jami’an mu bayan ya kawo yaron aka kulla ciniki kan Naira Dubu 150, shi kuma ya amince wajen karbar kudin ne muka cacime shi,” a cewar Hukumar ’yan sanda.
’Yan sanda sun bayyana cewa:”Wannan dai ba sabon abu ba ne ga ’yan asalin Jihar Kuros Riba, cdwa an dauko karamin yaro ko yarinya a kawo unguwar Hausawa a ce za a sayar.
Kuma Sarkin Hausawa ya kan jajirce kan duk wanda ya zo da sunan bata musu suna sai su sanar da hukuma. Kakakin rundunar ’yan sandan Kuros Riba, Hogan Bassey ya tababtar da aukuwarlamarin, inda ya bayyana cewa, suna ci gaba dabincike.