’Yan sanda sun kama wasu matasa masu yi wa mata fyade a Filato

A kokarinta na kawar da masu aikata miyagun laifuffuka Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta kama wasu matasa tara da take zargin sun gwanance wajen yi wa mata da kananan yara fade a sassan jihar. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Chris Olakpe ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da mutum bakwai daga cikin […]

’Yan sanda sun kama wasu matasa masu yi wa mata fyade a Filato

A kokarinta na kawar da masu aikata miyagun laifuffuka Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta kama wasu matasa tara da take zargin sun gwanance wajen yi wa mata da kananan yara fade a sassan jihar.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Chris Olakpe ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da mutum bakwai daga cikin mutum taran ga ’yan jarida a Jos.
Mista Chris Olakpe ya ce ana zargin wadannan matasa da shekarunsu ba su wuce 25 ba da yi wa wata yarinya ’yar shekara tara mai suna Christiana danlami fyade.
Ya ce matasan su ne Richard John da Zere Adam da Hamza Musa da Ugochukwu Raphael da Emmanuel Ibrahim da Sok Dabou, kuma ya ce rundunar tana ci gaba da bincike kan wannan al’amari.
Har ila yau Kwamishinan ya gabatar da wani boka mai suna Emmanuel Bala da ke zaune a kauyen Rim a karamar Hukumar Riyom da ke jihar da ake zarginsa da yi wa mace mai suna Ebelyn Ezekiel fyade.
Shi dai wannan boka ya yi wa matar fyaden ne a lokacin da ta je wurinsa neman magani.
Haka kuma Kwamishinan ya gabatar da wani mutum mai suna Abdullahi Adams mai shekara 31 da ake zargi da yi wa wata yarinya ’yar shekara bakwai mai suna Halima fyade. Ya ce ana zargin Abdullahi Adams ya daure hannun yarinyar ce tare da rufe bakinta a dakinsa ya yi mata fyaden.