’Yan sanda sun kama ’yan fashi 11 a Jigawa
Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta damke matasa 11 da ake zargi da laifin fashi da makami a kananan hukumomin Dutse da babura da Birnin Kudu.Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Theophilus Kayode wanda ya nuna wa manema labarai wadanda ake zargin a Dutse, ya ce a babura an kama matasa biyar da suka hada da […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta damke matasa 11 da ake zargi da laifin fashi da makami a kananan hukumomin Dutse da babura da Birnin Kudu.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Theophilus Kayode wanda ya nuna wa manema labarai wadanda ake zargin a Dutse, ya ce a babura an kama matasa biyar da suka hada da Ahmadu Musa da ake kira Gambo da Yahaya Ado da Haruna Idi da Haruna Sule da Sunusi Yahaya, yayin da abokan ta’asarsu suka ranta a na kare amma a kokarin ’yan sanda na su kama su, suka samu raunukan da suka yi sanadin mutuwarsu.
’Yan sandan sun ce sun gano kananan bindigogi kirar gida da wukake da guraye da wayoyin hannu hudu da ake zaton wadanda ake zargin sun kwace ne daga jama’a.
Mista Theophilus ya ce sun samu nasarar kama wadanda ake zargin ne sakamakon bayanan da suka samu daga wadanda suka taba yi wa fashi a hanyar babura zuwa Kanya Babba. Ya ce wadanda ake zargin sun jima suna addabar hanyar babura zuwa Kanya da Gidan Lage da kuma Garki.
Ya ce a karamar Hukumar Birnin Kudu ’yan sanda sun kama wasu matasa hudu da suka hada da Muhammed Isma’ila da Abdullahi Ruwali da Umar Da’u da kuma Balarabe Muhammed dukkansu mazauna kauyen Lirinde da ke karamar hukumar ne, bisa zarginsu da fashi da makami.
Ya ce, wadanda ake zargin sun shiga gidan wani mai suna Malam Ya’u Muhammed da miyagun makamai da suka hada da wukake suka yi masa barazanar sannan suka kwace masa Naira dubu 193 da 400, inda binciken ’yan sanda ya gano mutanen hudu.
Kwamishinan ya ce ’yan sanda sun kama wani matashi da ya kware wajen yin jabun takardu da kuma fashi, inda ya yi barazanar halaka wani matashi a gidansa da ke Takur a karamar Hukumar Dutse.
Matsahin mai suna Muhammed A. Abdulahi ya ce shi mutumin Nasarawa ne a Jihar Nasarawa kuma mahaifinsa dan sanda ne da ya bata ya fito nemansa. Ya musanta zargin, inda ya ce bai aikata fashi da makami ba, kazafi kawai aka yi masa.
Daga Umar Akilu Majeri, Dutse