’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe
Rundunar ta ce za ta gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu, da zarar ta kammala bincike.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma yunƙurin satar mutane a Ƙaramar Hukumar Dukku a jihar.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana suyane waɗanda aka kama.
Sunayensu sun haɗa da Muhammad Musa Korau (mai shekara 28), Aisha Jibir (mai shekara 28), Musa Haruna (mai shekara 35), Musa Muhammad Ajiya (mai shekara 24), Saleh Wammi (mai shekara 42), da Abubakar Isah (mai shekara 45).
A cewarsa, wani mutum mai suna Muhammad Ibrahim, mai shekara 29 ne, ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na Dukku a ranar 5 ga watan Janairu, 2025.
Ibrahim, ya ce wasu mutum 10 ɗauke da makamai sun kutsa gidansa da safiyar ranar 4 ga watan Janairu.
Sun firgita shi, sannan sun ƙwace masa babur ƙirar Bajaj Boxer mai launin ja wanda kuɗinsa ya kai Naira miliyan ɗaya da dubu ashirin (₦1,020,000).
Har ila yau, ya ce sun kwashe masa wasu kuɗi har Naira miliyan biyu da dubu dari bakwai da arba’in (₦2,740,000).
DSP Abdullahi, ya ce jami’an ’yan sanda sun fara bincike cikin gaggawa bayan samun rahoton, kuma ta hanyar bayanan sirri suka kama waɗanda ake zargi.
Daga cikin abubuwan da aka samu hannunsu akwai waya ƙirar Techno.
Sai dai, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, Aisha Jibir, ta musanta hannunta a lamarin.
Ta ce ba ta san komai ba, kuma ta ce ’yan sanda sun kama ta ne a gidanta ba tare da wani dalili ba.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike, kuma za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.