‘Yan sanda sun kama ‘yan fashi 7 a Benuwe

Hukumar ‘yan sandan jihar Benuwe ta kama mutane bakwai da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a hanyar Aliade dake karamar hukumar Gwer ta Gabas a jihar. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar DSP Moses Yamu ne ya sanar da hakan a yau Talata, bayan wani farmaki da ‘yan fashin suka kai a yankin Ikpayongo […]

‘Yan sanda sun kama ‘yan fashi 7 a Benuwe

Hukumar ‘yan sandan jihar Benuwe ta kama mutane bakwai da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a hanyar Aliade dake karamar hukumar Gwer ta Gabas a jihar.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar DSP Moses Yamu ne ya sanar da hakan a yau Talata, bayan wani farmaki da ‘yan fashin suka kai a yankin Ikpayongo dake Aliade, jami’an tsaron FSARS ne suka kama wadanda ake zargin ‘yan fashi ne.

Wadanda ake zargin sun hada da: Terdoo Nyamtaver dan shekara  27, Atondu Nyam dan shekara 20, Takari Anja dan shekara 43, Terkimbi Akighir dan shekara 35, Msughter Abe alias Don shayo dan shekara 21 da kuma  Msughter Tyosula alias Sunny dan shekara 22, duk kansu ‘yan garin Mba-Amande a Gwer ta Gabas.