’Yan sanda sun kama ’yan fashi bakwai a Jihar Sakkwato

’Yan sanda a Jihar Sakkwato sun kama ’yan fashi da makami bakwai, inda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Lawal Gambo ya nuna wa manema labarai ’yan fashin a ranar Talatar da ta gabata.Kwamishina Gambo ya ce “Mun kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban, mutum hudu an kama su ne dauke da takobi da […]

’Yan sanda sun kama ’yan fashi bakwai a Jihar Sakkwato
’Yan sanda sun kama ’yan fashi bakwai a Jihar Sakkwato

’Yan sanda a Jihar Sakkwato sun kama ’yan fashi da makami bakwai, inda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Lawal Gambo ya nuna wa manema labarai ’yan fashin a ranar Talatar da ta gabata.
Kwamishina Gambo ya ce “Mun kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban, mutum hudu an kama su ne dauke da takobi da gatari da sanda da hular rufe fuska, a kauyen Inguzo a karamar Hukumar Wurno inda ake zargin sun tafi yi wa wani dan kasuwa fashi.
Ya ce dayan mai suna Malam Yusuf an kama shi ne a kauyen Madagala-Ruwa a karamar Hukumar Tangaza lokacin da suke kokarin yi wani mutum fashi, kuma a yayin artabun ne aka kashe dan uwansa kuma an kama su dauke da bindiga.
Kwamishinan ya ce mutum biyu kuma an kama su ne su a Jihar Kano bayan sun yi fashi a kasuwar Ilela, inda aka yi nasarar kama su ta hanyar wayar salula.
Kwamishina Lawal ya sun samu nasarar kama ’yan fashi ne bisa hadin kan da al’ummar jihar ke ba su, inda ya yi gargadin cewa duk mai mugun shiri ko hali kada ya je jihar domin ba zai samu nasara ba.