’Yan sanda sun kama ’yan fashi da makami 9 a Jihar Oyo
Rundunar ’yan sanda a Jihar Oyo ta kama wasu ’yan fashi da makami su 9 a wurare daban-daban, wadanda suka yi wa ’yan jarida tabbataccen bayanin sun aikata laifukan da suka kai ga kama su. Biyu daga cikin barayin, Olatunbosu Ojetunde da Wasiu Folarin, an kama su ne bayan sun kwace tirela mai dauke da […]

Rundunar ’yan sanda a Jihar Oyo ta kama wasu ’yan fashi da makami su 9 a wurare daban-daban, wadanda suka yi wa ’yan jarida tabbataccen bayanin sun aikata laifukan da suka kai ga kama su. Biyu daga cikin barayin, Olatunbosu Ojetunde da Wasiu Folarin, an kama su ne bayan sun kwace tirela mai dauke da buhunan waken soya a kan hanyar ‘Espress’ ta Ife zuwa Ibadan, yayin da suka raunatar da direban suka karkatar da akalarta zuwa wata hanya daban. Amma rundunar tsaro ta Skynet da ke sintiri, wacce Sufeto Muhammed Abubakar ke jagoranta, ta yi nasarar kama su tare da karamar mota kirar Mazda da suke amfani da ita wajen aikata danyen aikin nasu da wata sharbebiyar adda da jini a jikinta. An kama su ne a kan hanyar Sango zuwa Eleyele cikin birnin Ibadan.
Da yake nuna ’yan fashin, a ranar Litinin a ofishinsa, Kwamishinan ’yan sanda Muhammed Abdulkadir Indabawa, ya nuna wasu 3 daga cikinsu da suka shiga cikin gida dan majalisar dokoki ta Jihar Oyo, Mista Waliu Adekunle a garin Oyo, suka yi awon gaba da kudade da gwala-gwalai da wayoyin salula. barayin masu suna Isma’il Oluwasegun, mai shekaru 26 da Amodu Garba, mai shekaru 20 da Oluwaseyi Oyenirang, wadanda dukansu sun yi ikirarin aikata laifin.
Haka nan Kwamishinan ya nuna wasu mutum biyu, Ibitoye Modesola da Tolulope Ojebode da aka kama su dauke da bindigogi 2 kirar AK 47 da harsasai 15 da hula irin ta sojoji da safar boye fuska, bayan sun yi wa gidan wani mutum mai suna Isma’ila, a garin Moniya, dirar mikiya suka sace dukiya da kadarori.
Haka kuma ASP Aminu Mustapha ya jagoranci wata rundunar sintiri da suka yi nasarar kama Samuel Caleb da Segun Famawode da raunukan harbin bindiga a cinya. Bayan binciken kwakwaf ne suka tabbatar da cewa sun samu raunukan ne a lokacin da suke kokarin tserewa daga wani hari da suka kai a gidan wata mata mai suna Alhaja Mufuliat Adebayo, a unguwar Idi Ori a garin Sasa, raunukan da suka yi sanadin mutuwarsu daga baya.
Kwamishina Indabawa, ya ce suna nan suna kokarin kama wani mai suna Fasola da ke zaune a unguwar Sabo, wanda aka gano cewa shi ne mutumin da yake karbar kayan sata daga hannun barayi.
Dukkan wadanda ake tsare da su za a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala bincike, inji Kwamishina Indabawa.