‘Yan sanda sun kama ‘yan fashi da masu satar mutane a Kebbi
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutum 10 a sassan jihar da ake zargi da fashi da makami da satar mutane domin neman kudin fansa. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi, Ibrahim M. Kabiru ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake gabatar da wadanda ake tuhumar ga manema labarai ban a Hedikwatar […]

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutum 10 a sassan jihar da ake zargi da fashi da makami da satar mutane domin neman kudin fansa. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi, Ibrahim M. Kabiru ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake gabatar da wadanda ake tuhumar ga manema labarai ban a Hedikwatar ’Yan sandan Jihar da ke Birnin Kebbi.
Kwamishinan ya ce rundunar ta lashi takobin ci gaba da dakile miyagu a jihar, kuma zai dauki matakin da ya kamata domin kara wa jami’ansa kwarin gwiwa wajen samar wa mutanen jihar damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
“Daga lokacin da aka kawo ni Jihar Kebbi na lashi takobin sa kafar wando daya da dukan masu tayar da zaune-tsaye, kuma na yaba hadin kai da kungiyoyi da daidaikun jama’a ke ba rundunar, don dakile miyagun da ke barazana ga rayuwar jama’a,” inji shi.
Kwamishinan ’Yan sandan ya ce cikin wadanda aka kama akwai Mohammed Altine Barbuje dan kimanin shekara 29 da Umaru Sajo da Mohammed Nasamu da Shu’aibu Abubakar da Sadik Usman da Babangida Jega, dukansu an kama su da bindigogi da alburusai, an kuma kama su ne a garuruwan Bunza da Tungar Bello da Barbuje da Jega da Masama.
Kwamishinan ya ce wadansu daga cikin mutanen su ne suka sace Limamin Senchi Alhaji Mode Senchi a bara, ba a samu sa’ar kama su ba sai a kwanan nan. Ya ce rundunarsa ta yi karin girma ga ’yan sanda 766 daga ciki 181 sun samu karin girma daga Saje zuwa Sufeto, sai 585 daga Kofur zuwa Saje.
A karshe Kwamishina Ibrahim M. Kabiru ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu kan taimakon da yake ba su a matsayinsa na babban jami’in tsaro na Jihar Kebbi.