’Yan sanda sun kama ’yan fashin da suka addabi yankin Kuri
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta samu nasarar cafke wasu matasa biyu da ake zargin sun addabi mutanen yankin Kuri da fashi da makami.Matasan Mu’azu Sale da Abdullahi Mumini mai inkiya da Mado, ana zargin sun kware wajen fashi da makami ta amfani da babur kirar Bajaj a kan hanyar Balanga zuwa kauyukan Kuri.Da yake […]

Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta samu nasarar cafke wasu matasa biyu da ake zargin sun addabi mutanen yankin Kuri da fashi da makami.
Matasan Mu’azu Sale da Abdullahi Mumini mai inkiya da Mado, ana zargin sun kware wajen fashi da makami ta amfani da babur kirar Bajaj a kan hanyar Balanga zuwa kauyukan Kuri.
Da yake yi wa manema labarai bayani game da ’yan fashin Kakakin Rundunar DSP Fwaje Atajiri, ya ce Mu’azu Sale, shahararren dan fashi ne a yankin kuma shi Abdullahi Mumimi shi ke samar musu da bindiga da makaman da suke fashi da su.
Ya ce kafin su samu nasarar kama wadanda ake zargin sai da suka yi amfani da dabaru da bayanan da suka samu daga jama’ar yankin suka kama su cikin dare. Ya ce sun bi su suna kan babur dinsu da suka fadi ne ’yan sandan suka kama su tare da babur din da wata bindiga mai baki biyu.
’Yan sandan sun kuma kama wasu matasa 27 da suke zargin batagari ne da suka kware wajen aikata miyagun laifuffuka a jihar da suka hada da satar babura da fasa motoci da sauransu. DSP Fwaje Atajiri, ya ce an kama su ne a unguwannin Tudun-Wada da Arawa da Kagarawal a fadar jihar, sai kuma wadanda aka kama a Unguwar Idi dauke da miyagun makamai bayan sun guntule wa wasu mutum biyu yatsun hannu sun sassare su a jiki.