‘Yan sanda sun kama ‘yan kungiyar asiri 86 a Legas

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta kama mutum 86 da take zargin ’yan kungiyar asiri ne a yankin Ikorodu da Ijede a wani farmaki da ayarin musamman da ke yaki da miyagun ayyuka da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Hakeem Odumosu, ya kaddamar. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa […]

‘Yan sanda sun kama ‘yan kungiyar asiri 86 a Legas

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta kama mutum 86 da take zargin ’yan kungiyar asiri ne a yankin Ikorodu da Ijede a wani farmaki da ayarin musamman da ke yaki da miyagun ayyuka da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Hakeem Odumosu, ya kaddamar.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan sandan sun kama wadanda ake zargi ’yan kungiyar asiri ne 21 a Unguwar Adamo da ke yankin Imota a Ikurodu, “Wadannan ’yan kungiyar asirin da muka kama su ne ke tada hankalin al’ummar yankin ta hanyar miyagun ayyukansu, an yi nasarar kama su ne ta amfani da bayanan sirri tare da rundunar hadaka. A yankin Ijede an kama ’yan kungiyar asiri 65, wadanda aka same su da kananan bindigogi 11.

Ya ce, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na tada hankalin al’ummar Ikorodu tare da yi musu fashi da makami.

Ya ce wadanda ake zargin mambobin kungiyar asiri ta Aiye da Eiye ne wadanda ba sa ga maciji da juna, inda ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci shari’a.