’Yan sanda sun kama ’yan Shi’a 115 a Abuja
Rundunar ’yan sandan birnin tarayya na Abuja sun kama membobin kungiyar gwagwarmayar musulunci bayan arangamar da aka yi tsakanin membobin da ’yan sanda a Abuja jiya. An ruwaito cewa wani memba na kungiyar ya rasa ransa yayin da harsashi ya same shi a lokacin da ’yan sanda ke kokarin tarwatsa taron membobin kungiyar IMN […]
Rundunar ’yan sandan birnin tarayya na Abuja sun kama membobin kungiyar gwagwarmayar musulunci bayan arangamar da aka yi tsakanin membobin da ’yan sanda a Abuja jiya.
An ruwaito cewa wani memba na kungiyar ya rasa ransa yayin da harsashi ya same shi a lokacin da ’yan sanda ke kokarin tarwatsa taron membobin kungiyar IMN wadanda suka taru a shataletalen Unity Fountain da ke Maitama a Abuja inda suke zaman dirshen don ganin an sako shugabansu Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Wata majiya ta ce ’yan sanda sun yi kokarin tarwatsa masu zanga-zanga don kada lamarin ya yi kamari ta yadda za a karya doka da oda yayin da shugaban rundunar sojojin Najeriya ke yin taro a babban otel din Transcop Hilton wanda ke daura da wurin da lamarin ya auku.
Wani ganau ya ce membobin kungiyar IMN sun ki yarda ’yan sandan su tarwatsa su inda ’yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa a kansu inda su kuma suka rika jifan ’yan sanda da duwatsu suka rika dukan motar sulke ta ’yan sandan da sanduna.