’Yan sanda sun karyata labarin bullar ’yan boko haram a Jihar Oyo
Rundunar ’yan sanda a Jihar Oyo ta karyata jita-jitar da ake yayatawa a shekaranjiya Laraba cewa ’yan boko haram su 18 dauke da bindigogi kirar AK 47 sun kashe ’yan sanda 9 da mutum 11 a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.Sanarwar, wadda ke dauke da sanya hannun Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Oyo, […]
Rundunar ’yan sanda a Jihar Oyo ta karyata jita-jitar da ake yayatawa a shekaranjiya Laraba cewa ’yan boko haram su 18 dauke da bindigogi kirar AK 47 sun kashe ’yan sanda 9 da mutum 11 a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
Sanarwar, wadda ke dauke da sanya hannun Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Oyo, SP Olabisi Okuwobi-Ilobanafor ta shawarci jama’a su daina sauraron jita-jita maras kan gado kuma su daina taimaka wa masu baza ta. “Wani hadari da ya auku a kan wannan hanya da ya shafi wata tirela dauke da buhunan alkama, ’yan sanda da jami’an kiyaye hadurra sun je domin hamzarta kawar da tarkacen kaya daga kan hanya domin sauran motoci su samu saukin wucewa ne”, inji sanarwar.
A daidai wannan lokaci ne rundunar ’yan sandan ta yi wata ganawa da shugabannin Hausawa da Fulani da wakilan kungiyoyin manoma da suka bayar da shawarwarinsu dangane da matsalar tabarbarewar tsaro a kasar nan.
Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Mista Clement Adoda, shi ne ya wakilci Kwamishina Muhammed Inda-bawa a wajen wannan ganawa, wadda aka yi a zauren taro na hedkwatar ’yan sanda da ke Eleyele a Ibadan. Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Mai Yasin da Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmed dahiru Zungeru da wakilin Sarkin Iseyin, Basorun Oyegbenle Adelodun da Oniseri na Iserin Ile, Oba Lawrence Taiwo Adeyemi da Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Jihar Oyo, Alhaji Yakubu Bello sun bayar da muhimman shawarwari a game da hanyoyon da za su taimaka wajen yin riga-kafin bullar ’yan boko haram a cikin jama’a da hanyoyin shawo kan matsalar fadace-fadace a tsakanin manoma da makiyaya.
Bayan sauraron shawarwarin ne Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda Clement Adoda da takwaransa Musa Kimo, suka nemi jama’a su koma gidajensu tare da kyakkyawar lura da zirga-zirgar baki a cikinsu kuma su tabbatar da cewa sun hanzarta sanar da shugabanninsu bullar wani abu da ba su saba gani ba.
Sarkunan Hausawa da Fulani da shugabannin kungiyoyin Izala da darika da shugabannin kungiyoyin ’yan kasuwa daga sassa daban-daban na jihar sun halarci ganawar ta shekaranjiya Laraba.