’Yan sanda sun kashe dan bumburutu a Kaduna
Sakamakon hana sayar da man fetur a jarkoki da gala-galan da ake kira bumburutu da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi, wadansu ’yan sanda sun bindige wani dan bumburutu a ranar Alhamis da ta wuce da misalin karfe 2:00 na dare lokacin da suke kan hanyar zuwa sayo mai a gaba da Marabar Jos da ke […]
Sakamakon hana sayar da man fetur a jarkoki da gala-galan da ake kira bumburutu da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi, wadansu ’yan sanda sun bindige wani dan bumburutu a ranar Alhamis da ta wuce da misalin karfe 2:00 na dare lokacin da suke kan hanyar zuwa sayo mai a gaba da Marabar Jos da ke a jihar.
Abokin mamacin wanda shi yake tuka motar da suke ciki, mai suna Ibrahim ya ce sun fita da daddare ne domin zuwa sayo man fetur sakamakon hana sayar da mai da gwamnatin jihar ta yi a fadin jahar. “Marigayi dan Agro ne ya ce da ni in dauki shi mu je mu sayo man fetur a can gaba da Mararrabar Jos da daddare. Muna kan hanyar tafiya sai muka hadu da wadansu ’yan sanda da suka tambaye mu inda za mu je muka fada musu za mu je sayo man fetur ne. Daga nan sai muka ba su Naira dubu daya suka bar mu muka wuce. Muna cikin tafiya sai muka hadu da ’yan banga bayan sun tsayar da mu sai muka fada musu inda za mu je, suka ce ai ba sai mun yi nisa ba akwai wani gidan mai da ke da sauki kusa da inda muke. Muka juya mota da nufin tafiya can. Muna tafiya sai muka hango ’yan sanda a gabanmu suna haskamu da fitilar hannu. Amma sai muka wuce su ba tare da mun tsaya ba. Da suka ga haka sai suka biyo mu a guje. Da ma mu uku ne a cikin motar sai jarkokin man da ke cikin motar. Ganin ba mu tsaya ba, sai na ji sun yi harbi. Na ce da marigayi ko dai in tsaya ne sai ya ce a’a mu ci gaba da tafiya yana ganin harbin ban tsaro suke yi mana. Suka sake harbi na bayan sai ya kwanta can sai na sake jin karar harbi daga nan ne sai na ji dan Agro ya kwanto jikina jini na zuba,” inji shi.
Ya ce da ya duba sai ya ga sun same shi a keya ganin haka sai suka tsayar da mota. “Da ’yan sandan suka ga sun kashe shi, sai suka ce da ni ku barayi ne na ce a’a, daga san sai suka ce in kai shi asibiti. Su kuma sai suka shiga cikin motarsu suka yi tafiyarsu,” inji shi.
Mahifiyarsa marigayin wadda ba ta ambaci sunanta ba, da ke Unguwar Shanu ta nuna bakin ciki kan yadda aka kashe danta ba tare da ya aikata wani laifi ba. “Ba su rigaya sun sayo fetur din ba suka harbe shi. Kuma yaron nan dai kokari yake ya nemi halaliyarsa. Ina yi masa addu’ar Allah Ya gafarta masa zunubansa,” inji ta.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Zubairu Abubakar bai amsa waya ba lokacin da wakilinmu ya kira shi, balle a ji bayani daga bangarensu.