’Yan Sanda sun kashe kusan mutum 1,000 bara a Amurka – Rahoto

Wani rahoto na musamman da kamfanin dillacin labarai na AFP ya rairayo ya nuna yadda ’Yan Sandan Amurka suka hallaka kusan mutum 1,000 ba gaira ba dalili bara kamar yadda suka samu alkaluman daga Washington Post. ’Yan Sandan sun yi wa mutum 987 kisan gilla bara, wanda ya nuna an samu kari a kan 963 […]

’Yan Sanda sun kashe kusan mutum 1,000 bara a Amurka – Rahoto

Wani rahoto na musamman da kamfanin dillacin labarai na AFP ya rairayo ya nuna yadda ’Yan Sandan Amurka suka hallaka kusan mutum 1,000 ba gaira ba dalili bara kamar yadda suka samu alkaluman daga Washington Post.

’Yan Sandan sun yi wa mutum 987 kisan gilla bara, wanda ya nuna an samu kari a kan 963 da aka samu a shekarar 2016 kamar yadda rahoton ya nuna.

Jaridar ta dade tana nuna yadda ’Yan Sanda suke kisan gilla a kasar ta hanyar bibbiyan rahotanni da ke fitowa daga bangarori da yawa na kasar, da alkaluma da suke samu daga kafafen sada zumunta na zamani tun shekarar 2015.

Yadda ’Yan Sandan suke amfani da karfin tsiya wajen gudanar da aikinsu yana janyo cece-kuce, musamman yadda suke kisan gilla ga mutane farin hula wadanda ba sa dauke da makami.

Alkaluman sun nuna yadda ’Yan Sanda suka kashe wasu ’yan yankin Afirka su 19, sannan kuma sun kashe 17 a shekarar 2016, sannan na shekarar 2015 ya fi yawa inda suka kashe mutum 36 ’yan asalin Afirka din.

Sannan kuma rahoton ya nuna cewa ana yi wa bakaken fata kisan gilla ba gaira ba dalili. Kashi 22 na mutanen da aka kashe bakaken fata ne, wadanda suka hada da masu daukan makami da wadanda babu ruwansu.

Hakanan kuma rahoton ya nuna cewa ’Yan Sanda sun kashe mutum 68 wadanda ba sa dauke da makami bara, a shekarar 2016 kuma sun kashe 51, sannan kuma mutum 94 ne suka kashe a shekarar 2015.

Babban Jami’in gudanarwa na Hukumar Binciken Gudanarwar ’Yan Sanda, Chuck Wedler, ya ce “Yanayin yadda ake koke a kan yadda ’Yan Sanda suke kashe mutane ya sanya dole ’Yan Sandan su rika kula sosai.”

Alkaluman kuma sun nuna cewa mutum 735 da ‘Yan Sandan suka kashe suna dauke ne da makamai irinsu wukake ko bindigogi da dai sauransu, wanda ya nuna an samu kari a kan na shekarar 2016 na 693.

Hakanan kuma a bangaren ’Yan Sandan an kashe musu jami’ai 46 bara, a shekarar 2016 kuma an kashe musu jami’ai 66 ne, wanda ya nuna an samu kari ke nan.

Harbe-harbe da ’Yan Sanda suke yi a kasar Amurka ya fi kamari idan aka kwatanta da wasu kasashen da suka cigaba kamarsu.

Misali, alkaluma da kungiyar Binciken Burtaniya ya nuna cewa an kashe mutum shida ne kawai a shekarar 2016 a Burtaniya. Sannan wani bincike da Jaridar Berlin Tageszeitung ta buga ya nuna cewa na kashe mutum 13 ne kawai a shekarar 2016.