‘Yan sanda sun kashe mai garkuwa da kama mutum 46 a Edo
Hukumar ‘yan sanda a jihar Edo sun kashe wani da ake zargin mai yin garkuwa da mutane ne don karbar kudin fansa tare da tsare masu laifin da ake zarginsu da yin garkuwa su 46. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo Mista Johnson Kukumo, ne ya bayyana hakan a wajen taron manema labarai da aka yi […]
Hukumar ‘yan sanda a jihar Edo sun kashe wani da ake zargin mai yin garkuwa da mutane ne don karbar kudin fansa tare da tsare masu laifin da ake zarginsu da yin garkuwa su 46.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo Mista Johnson Kukumo, ne ya bayyana hakan a wajen taron manema labarai da aka yi ranar Talata a Benin.
Ya ce, jami’an ‘yan sanda sun kwato makamai 126 daga hannun wadanda ake zargin.
A cikin wadanda aka kama a kwai mutum 17 da ake zarginsu da yin garkuwa da fasto a unguwar Urhonigbe kusa da Agbor da ke jihar Delta.