’Yan sanda sun kashe masu laifi 9 da rasa jami’ai 6 a Abuja

Kwamishinan ‘yan sanda na Babban Birnin Tarayya Abuja, Miller Dantawaye ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a

’Yan sanda sun kashe masu laifi 9 da rasa jami’ai 6 a Abuja

Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya ta bayyana cewa, an kashe ’yan fashi da makami guda tara a yayin artabu da ‘yan sanda, yayin da jami’an ‘yan sanda shida suka rasa rayukansu a bakin aiki tsakanin Oktoba da Disamba 2025.

Kwamishinan ‘yan sanda na Babban Birnin Tarayya Abuja, Miller Dantawaye ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan da ke Abuja.

Kwamishinan, ya gabatar da sakamakon da hukumar ta samu na watanni uku na karshen shekarar 2025.

A cewar Dantawaye, an kashe masu laifin ne a yayin da ake gudanar da ayyukan yaƙi da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami, bayan da jami’an ‘yan sanda suka yi musayar wuta a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa ko kuma sace wasu jama’a.

“A yayin da ake gudanar da wasu ayyuka masu matuƙar haɗari a lokacin, musamman yaƙi da garkuwa da mutane da kuma daƙile ayyukan fashi da makami, an kashe mutane tara da ake zargin na ɗauke da makamai bayan sun yi musayar wuta da jami’an ‘yan sanda a yayin da suke ƙoƙarin tserewa ko kuma yin garkuwa da wasu,” in ji shi.

Ya ce, tsawon lokacin da ake bitar lamuran ya kuma bayyana irin asara mai raɗaɗida aka yi, domin jami’an ’yan sanda shida da aka kashe sun yi rawar gani yayin da suke gudanar da ayyukansu