‘Yan sanda sun kashe mutum 80 a Kenya

Wata kungiyar kare hakkin bil-adama a kasar Kenya, mai suna Haki Africa, ta ce ‘yan-sanda sun kashe mutane fiye da 80 a cikin yanayi mai daure kai a yankin da ke kusa da gabar ruwa cikin shekaru hudu da suka gabata. Hukumomi na zargin yawancin mutanan ne da kasancewa mambobin kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin Islama.Daraktan […]

‘Yan sanda sun kashe mutum 80 a Kenya
‘Yan sanda sun kashe mutum 80 a Kenya

Wata kungiyar kare hakkin bil-adama a kasar Kenya, mai suna Haki Africa, ta ce ‘yan-sanda sun kashe mutane fiye da 80 a cikin yanayi mai daure kai a yankin da ke kusa da gabar ruwa cikin shekaru hudu da suka gabata.

Hukumomi na zargin yawancin mutanan ne da kasancewa mambobin kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin Islama.
Daraktan zartaswa na kungiyar, Hussein Khalid, ya ce adadin ma ka iya fin haka, domin wasu iyalai na fargabar fitowa su bayyana abin da ya faru da ‘yan uwansu.
kungiyar ta ce wadanda lamarin ya rutsa da su, an kashe su ne lokacin dirar mikiya kan masu zanga-zanga da kuma wasu taruka a inda ake zargin ana cusawa matasa tsattsauran ra’ayi.
Wata hukumar sa ido kan ‘yan sanda ta ce ana binciken jami’ai 300 bisa zargin keta hakkin bil’adama.
A watan jiya ne Hukumomi a kasar suka ce ‘yan sanda sun kashe wasu da ake zargi ‘yan bindiga masu tsananin kishin Islama ne su hudu a kusa da iyakar kasar da Somaliya. Kwamishinan ‘yan sanda na Mandera ta Kudu, Fredrick Shisia ya ce ‘yan bindigan sun yi niyyar kai hari ne kan wani ofishin ‘yan sanda.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara