’Yan sanda sun kashe wani matashi a Zariya

A ranar Litinin da ta gabata ne mutanen Unguwar Daurawa da ke Muchiya Sabon-Gari Zariya suka tashi da juyayin rashin wani matashi dan unguwar da ake zargin ’yan sanda da kashe shi cikin dare ta hanyar duka.Matashin mai suna Muhammadu Murtala da aka fi sani da Bala Direban J5 mai kimanin shekara 25, ya rasa […]

’Yan sanda sun kashe wani matashi a Zariya

Marigayi Muhammad MurtalaA ranar Litinin da ta gabata ne mutanen Unguwar Daurawa da ke Muchiya Sabon-Gari Zariya suka tashi da juyayin rashin wani matashi dan unguwar da ake zargin ’yan sanda da kashe shi cikin dare ta hanyar duka.
Matashin mai suna Muhammadu Murtala da aka fi sani da Bala Direban J5 mai kimanin shekara 25, ya rasa ransa ne ta hanyar dukansa da gora da ake zargin ’yan sandan da yi.
Mahaifiyar marigayin mai suna Hafsat Shehu ta shaida wa Aminiya cewa marigayin ya fita gida ne domin ya sayo tocila “To bayan na ba shi Naira 200 ya fita ne sai aka zo aka ce in zo in ga Bala ’yan sanda sun yi masa duka har sun karya masa kafadu, kuma jini yana ta zuba ta bakinsa da kunnuwansa, kuma duk jikinsa kwata,” inji ta.
Ta ce ashe ba shi kadai ba ne su biyu ne suka buga shi da abokinsa shi ma abokin nasa sun ji masa ciwo “Muka zo muka sa masa ruwa muka wanke kwata da wanke jinin jikinsa muka kwantar da shi daga nan mahaifinsa ya tafi ofishin ’yan sanda cikin dare domin jin yadda aka yi, da ya isa sai wadanda suka yi dukan suka musunta, daga nan sai babbansu ya biyo shi domin ya ga yadda aka yi da ya ga halin da marigayi Bala yake ciki sai ya fashe da kuka ya ce ya ya za a ce ba a bugi wannan bawan Allah ba, ku dai ba ku yi aikin da aka sa ku ba,” inji ta.
Mahaifiyar Murtala ta ce shugaban nasu na fita Bala ya cika, kuma da gari yawaye sai matasa suka fusata suka nufi ofishin ’yan sandan domin nuna fushinsu, shi kuma mahaifin yaron da dattawan unguwa suka nufi gidan hakimi domin shaida masa, ashe kafin su je hakimi ya samu labarin abin da ke faruwa sai suka hadu da shi a hanya tare da jami’an tsaro sun nufo gidan domin kwantar da hankalinsu da na jama’ar unguwar kuma suka dauki gawar suka nufi asibiti.
Wakilinmu ya ce masu zanga-zanga sun kone ofishin ’yan sanda da ke Muchiya, domin nuna fushinsu kan abin da ya faru kasancewar sun ce yaron da aka kashe yana cikin yara nagari.
 Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna bai samu nasara ba, domin ya buga masa waya bai dauka ba, kuma bai amsa sakon tes da ya aika masa ba.
Wata majiya a babban ofishin ’yan sanda na Zariya ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai babban jami’in ya shaida masa cewa wadanda suka yi wannan aika-aika ba ’yan sanda ba ne, ’yan banga ne da ’yan sandan sarauniya.  Ya ce idan kuma ’yan sanda ne suka aikata wannan lamarin to doka ba za ta bar su ba, su ma wadanda suka kona ofishin ’yan sandan sun dauki doka a hannu in an kama su dole a hukunta su.