’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai
Rundunar ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da yaƙi da laifuka a jihar.
Rundunar ’Yan sanda Jihar Binuwai sun kashe wasu da ake zargi ’yan fashi ne guda uku, yayin musayar wuta a wani artabu aka gudanar a sassa daban-daban na jihar cikin mako guda.
A cewar kakakin ’yan sandan jihar, DSP Udeme, an gudanar da ayyukan ne tsakanin 6 zuwa 12 ga watan Yuni, 2026.
- Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo
- Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram
Ya ce an gudanar da ayyukan ne bayan samun bayanan sirri da kuma sintirin haɗin gwiwa domin yaƙi da fashi da makami, sace-sace da kuma ayyukan ’yan daba.
Akwai gagarumin artabu da aka yi a kan hanyar Vaase zuwa Chito a Ƙaramar Hukumar Ukum, inda ’yan sanda suka yi musayar wuta da wasu ’yan bindiga.
A nan ne aka kashe uku daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunuka.
’Yan sanda sun ce sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47, bindigogi da aka ƙera a gida, harsasai, babur da wasu kayayyaki daga wuraren da lamarin ya faru.
A wasu ayyuka na daban, jami’an tsaro sun kama wasu da ake zargi da fashi da makami da kuma faɗan daba, sannan sun kai samame maɓoyar masu laifi a sassa daban-daban na jihar.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike, yayin da Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin tare da tabbatar da ci gaba da yaƙi da laifuka a jihar.