’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 5 a Kuros Riba

’Yan Sandar a Jihar Kuros Riba sun yi nasarar harbe wadansu ’yan fashi da makami su biyar a wata musayar wuta da aka yi a tsakaninsu da ’yan fashin lokacin da suke fashi a wani gidan mai da ke Layin Atu a Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu. Aminiya ta samu labarin cewa, sun nuna cewa […]

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 5 a Kuros Riba
’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 5 a Kuros Riba

’Yan Sandar a Jihar Kuros Riba sun yi nasarar harbe wadansu ’yan fashi da makami su biyar a wata musayar wuta da aka yi a tsakaninsu da ’yan fashin lokacin da suke fashi a wani gidan mai da ke Layin Atu a Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu.

Aminiya ta samu labarin cewa, sun nuna cewa ’yan fashin sun je wani gidan mai ne da tsakar rana suka umarci ma’aikata da mutanen da ke shan mai su kwanta rub-da-ciki.

Ana cikin haka ne kuma ’yan sanda suka samu labarin fashin, suka kawo dauki kuma a wannan artabun ne ’yan sandan suka samu nasarar kashe ’yan fashi hudu.

A ’yan kwanakin nan ana samun karuwar fashi da makami da kuma wadansu bata-gari da suke yi wa mutane fisge, lamarin da Hukumar ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba ta ce ba za ta lamunta ba, abin da ya sanya ta baza jami’anta cikin shirin ko-ta- kwana a kowane lungu da sakon jihar domin bayar da tsaro ga al’umma.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani, Kwamishina ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, Hafiz Muhammad Inuwa ya ce jami’ansa sun yi nasarar harbe wadansu ’yan fashi da makami su biyar da suka je yin fashi a wani gidan mai na Ubi da ke Layin Atu.

Ya ce a wannan musayar wutar an kashe hudu daga cikinsu yayin da dayan kuma ya rasu daga baya. Ya ci gaba da cewa jami’an nasa sun yi nasarar kwace bindiga kirar AK47 guda biyu na barayin da kuma makudan kudin da aka yi ciniki a gidan man da suka so sacewa.

Hafiz Inuwa ya bukaci al’ummar Jihar Kuros Riba su rika sanar wa ’yan sanda duk wata maboyar bata-gari da kuma duk inda suka ji wani motsin da ba su yarda da shi ba, domin ta haka ne zai iya taimaka wa rundunar ta kakkabe miyagu.Ya ce rundunar tasa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbbatar da tsaro da kuma hana duk wani dan ta’adda sararawa a jihar.