’Yan sanda sun kashe ’yan fashin mota har lahira
Jami’an ’yan sanda sun bindige ’yan fashi shida da suka yi kaurin suna wajen kwacen motoci a Jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom. Da yake nuna gawar ’yan fashin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, Amiengheme Andrew, ya ce dubun bata-garin ta cika ne a lokacin da suke fashi a kan hanyar Itu zuwa Uyo […]
Jami’an ’yan sanda sun bindige ’yan fashi shida da suka yi kaurin suna wajen kwacen motoci a Jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom.
Da yake nuna gawar ’yan fashin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, Amiengheme Andrew, ya ce dubun bata-garin ta cika ne a lokacin da suke fashi a kan hanyar Itu zuwa Uyo a ranar Juma’a.
“Bayan samun rahoto sai ’yan sandan rundunar SARS suka isa wurin su kuma ’yan fashin da ganin su sai suka bude wa jami’an wuta.
“A musayar wutar ce ’yan fashin suka samu raunuka amma bayan an kai su asibitin ’yan sanda da ke Uyo sai likitoci suka tabbatar cewa sun mutu”, inji shi.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce ’yan fashin na kan hayarsu ta sayar da motar wani likita da suka kwace ne ’yan sanda suka rutsa su.
Abubuwan da aka kwace daga’yan fashin sun hada da kananan bindigogi biyar, albarusai da kwanson harsasai da kayan sojoji da motar da suka yi fashin ta da sauransu.
Kwamishinan ’yan sandan ya gargadi bata-gari da suka hada da ’yan fashi da masu fyade da su tattara su bar jihar ko kuma su gamu da gamonsu.