’Yan Sanda Sun Kira Rikakkun ’Yan Daba 52 Sulhu a Kano
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya yi zama da masu ruwa da tsaki a Kwanar Dangora kan matsalar ’yan daba
’Yan sanda sun gayyaci wasu jagororin ’yan daba 52 domin yin sulhu da su a Karamar Hukumar Kiru ta Jihar Kano.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Hussaini Muhammadu Gumel ne ya sanar da hakan a wani zama da ya yi da masu ruwa da tsaki a yankin Kwanar Dangora da ke Karamar Hukumar Kiru.
Kwamishinan ya yi kira ga mahalarta zaman da su ba da hadin kai wajen samar da wanzajjen tsaron rayuka da dukiyoyi a karamar hukumar da ma Jihar Kano baki daya.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ruwaito shi yana cewa, mahalarta taron sun taimaka wajen gano manyan ’yan daba guda 52 da ake nema a yi sulhu da su, saboda suna da hannu wajen tayar da zaune tsaye a karamar hukumar.
- ’Yan bindiga sun kashe dan uwan amarya, sun sace mahalarta biki a Kaduna
- Masu riga da ƙaro na mana shisshigi a aikin tsaro a Gombe — Cibil Difens
CP Hussaini Gumel ya yaba wa sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki da shugaban karamar hukumar Kiru bisa hadin kan da suke ba wa rundunar wajen samar da kwanciyar hankali a Kwanar Dangora, Karamar Hukumar Kiru da ma Jihar Kano.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana cewa, rundunarsa a shirye take wajen yaki da kuma murkushe da duk wani nau’i na barazanar tsaro a fadin Jihar Kano.