’Yan sanda sun kubutar da matar da aka sace kwanakin baya

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kurosriba ta yi katarin kubutar da uwargida Comfort Bassey Udoenwang, da ke Layin Jesus, karamar Hukumar Kalaba ta kudu daga hannun wasu da ake zargi masu kama mutane suna yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa ne suka boye ta a kauyen Akpap Okoyong, karamar Hukumar Odukpani, bayan wani […]

’Yan sanda sun kubutar da matar da aka sace kwanakin baya

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kurosriba ta yi katarin kubutar da uwargida Comfort Bassey Udoenwang, da ke Layin Jesus, karamar Hukumar Kalaba ta kudu daga hannun wasu da ake zargi masu kama mutane suna yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa ne suka boye ta a kauyen Akpap Okoyong, karamar Hukumar Odukpani, bayan wani samame da jami’an sashen da ke yaki da masu kama mutane suna garkuwa da su da kuma masu aikata sauran nau’in tsageranci na rundunar.

Da yake yi wa Aminiya karin bayanin yadda aka yi har nasarar ta samu, Hafiz Muhammad Inuwa, Kwamishinan ’yan sandan jihar ya ce, “yadda aka yi ma har waccan nasara ta samu shi ne, jami’anmu ne aka kyankyasa wa maboyar kuma ba su yi kasa a gwiwa ba; suka garzaya suka yi sa’ar kubutar da matar, bayan barin wuta da aka yi tsakaninsu da wadanda suka yi garkuwar da ita. Daga ciki ma an kashe daya, sauran sun arce da raunuka a jikinsu.”

Ya ci gaba da cewa:  “Lokacin da masu laifin suka ga ’yan sanda sun tunkari maboyarsu sai suka bude musu wuta amma duk da haka sun yi ta maza, daya daga cikinsu mai suna Isaac Sabastine, dan asalin karamar Hukumar Obot Akara, Jihar Akwa Ibom da aka raunata sanadiyar musayar wutar, ya arce da raunuka jikinsa.”

An kama wani mai suna Elele Dabid, shi kuma jagoran masu garkuwar Ayi Etok ya arce da raunukan da ya samu sanadin musayar wutar da ’yan sanda.

Kayayyakin ta’addanci da aka samu wurinsu sun hada da karamar bindiga kirar gida babba da kuma karama, kayan ’yan sanda da kuma tsumman da suke rufe wa wanda suka kama fuska. An kuma gano wata mota kirar Toyota mai lamba ANA420 CK. Gawar wanda aka kashe a musayar wutar, an kai ta asibitin koyarwa na Jami’ar Kalaba, yayin da matar da aka kubutar tare da kayayyakinta, an ba ta, an kuma sada ta da iyalanta.

Daga nan kwamishinan ya kara jaddada aniyarsa ta ganin rundunarsa ta kakkabe bata-gari da kuma ci gaba da bayar da tsaro bakin gwargwado, ta yadda kowane mazaunin Jihar Kurosriba zai rika yin barci da saleba.