‘Yan sanda sun kubutar da mutum 6 da aka yi garkuwa a Katsina

Bayan musayar wuta tsakanin masu garkuwa da mutane da jami’an ‘yan sanda, an yi nasarar kubutar da mutum shida da aka yi garkuwa da su a jihar Katsina a jiya Laraba. Kakakin rundunar  ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce da a jiya Laraba ne da misalin karfe 12:30 na rana ya amsa […]

‘Yan sanda sun kubutar da mutum 6 da aka yi garkuwa a Katsina

Bayan musayar wuta tsakanin masu garkuwa da mutane da jami’an ‘yan sanda, an yi nasarar kubutar da mutum shida da aka yi garkuwa da su a jihar Katsina a jiya Laraba.

Kakakin rundunar  ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce da a jiya Laraba ne da misalin karfe 12:30 na rana ya amsa kiran wayar salula a kan cewa an wasu tawagar ‘yan bindigar dauke da bindigogi kirar AK47 sannan sun yi garkuwa da wasu mata da ke aiki a cikin wata gona a kauyen Mata-Mulki karamar Hukumar Batsari.

Rundunar ‘yan sanda karkashin Operation Puff Adder wanda shugaban ofishin ‘yan sandan Batsari DPO ne ya jagoranci jami’an ‘yan sandan aka kubutar wadanda aka ceto.