’Yan sanda sun kubutar da Turawan da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Rundunar ’yan sanda sun samu nasarar kubutar da ’yan kasashen waje hudu da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Kagarko zuwa Kwoi da ke cikin jihar Kaduna.   Wasu gungun ’yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan kasar Amurka biyu da ’yan kasar Kanada biyu a yammacin ranar Talatar da ta gabata a […]

’Yan sanda sun kubutar da Turawan da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Rundunar ’yan sanda sun samu nasarar kubutar da ’yan kasashen waje hudu da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Kagarko zuwa Kwoi da ke cikin jihar Kaduna.
 
Wasu gungun ’yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan kasar Amurka biyu da ’yan kasar Kanada biyu a yammacin ranar Talatar da ta gabata a kan hanyarsu ta zuwa Abuja don duba wasu wurare a garin Kafancan.
 
’Yan bindigar sun kashe ’yan sanda biyu da ke tsaron lafiyar ’yan kasashen wajen yayin da suke kokarin sace su.