’Yan sanda sun kubutar da yara uku da mai renonsu ta sace
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta ce ta kubutar da yara ukun da mai renonsu ta sace a makon da ya gabata daga gidansu da ke kan titin Lawanson a Jihar Legas. Yaran sun hada da Aderomola mai watanni 11 da Adedamola mai shekaru hudu da kuma Demola mai shekaru shida a duniya.Mai magana da […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta ce ta kubutar da yara ukun da mai renonsu ta sace a makon da ya gabata daga gidansu da ke kan titin Lawanson a Jihar Legas.
Yaran sun hada da Aderomola mai watanni 11 da Adedamola mai shekaru hudu da kuma Demola mai shekaru shida a duniya.
Mai magana da yawun rundunar, Kenneth Nwosu ya shaida wa Aminiya cewa wadanda suka yi garkuwa da yaran sun gudu sun bar su saboda matsawar da ’yan sanda suka yi musu.
Ya bayyana cewa ’yan sanda sun kwashi yaran daga wani gini da ba kowa a cikinsa a yankin unguwar Akowonjo da ke Jihar Legas.
“Ina mai tabbatar maka da cewa ’yan sanda sun ceto yaran. A yanzu haka ana duba lafiyarsu a asibitin ’yan sanda da ke Ikeja, iyayensu suna tare da su a asibitin. Da zarar likitoci sun tabbatar da koshin lafiyarsu za a sallame su don su tafi gida tare da iyayensu.”
Kodayake mai magana da yawun ’yan sandan bai bayyana ko an biya kudi kafin a saki yaran ba to sai dai mahaifin yaran Lere Orekoye ya tabbatar da cewa an samo yaran kuma suna tare da su amma kuma bai yi karin haske dangane da ko an biya kudi ko ba a biya ba kafin a sake su.
Lere ya bayyana cewa Mary ta yaudare su inda har hada su ta yi da wasu ’yan uwanta na karya, wadanda suka tsaya mata kuma suka cike dukkannin takardun yarjeniyar da aka yi kafin a dauke ta aikin renon yaran.
Daga bisani ya yaba wa dukkanin wadanda suka taimaka wajen ganin yaran sun kubuta daga wurin wadanda suka yi garkuwa da su.
Iyayen yaran sun hadu da mai renonsu mai suna Mary Akinloye ta kafar sadarwar saye da sayarwa mai lakabin OLd amma cikin awa 24 da fara aikin renon sai ta sace su tare da yin garkuwa da su da taimakon abokan huldarta.
Daga bisani sai ita da abokanenta suka kira iyayen yaran ta wayar salula suka bukaci su ba su Naira miliyan 15 kafin su saki yaran.
Amma sai suka rage kudin zuwa Naira miliyan sha uku bayan rokon da iyayen yaran suka rika yi musu na neman ragi.
Sai dai sun yi barazanar kashe yaran idan ba a biya kudin da suka nema ba.