’Yan sanda sun kwato bindigogi 3,250 cikin mako shida

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce ta kwato bindigogi sama da 3,250 daga kungiyoyin banga da daidaikun mutane a sassan kasar nan cikin mako shida. Wannan ya biyo umarnin da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Ibrahim Kpotun Idris ya bayar ne a ranar 21 ga Fabrairun da ya gabata cewa duk wadanda suka mallaki […]

’Yan sanda sun kwato bindigogi 3,250 cikin mako shida

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce ta kwato bindigogi sama da 3,250 daga kungiyoyin banga da daidaikun mutane a sassan kasar nan cikin mako shida.

Wannan ya biyo umarnin da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Ibrahim Kpotun Idris ya bayar ne a ranar 21 ga Fabrairun da ya gabata cewa duk wadanda suka mallaki bindigogi ba tare da izini ba su mika su ga ’yan sanda ko su fuskanci shari’a.

Kakakin Rundunar ta kasa Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, Jimoh Moshood, ya bayyana haka ga manema labarai a Hedkwatar ’Yan sanda ta kasa da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata lokacin baje bindigogin da kwamitin cika aiki na hadin gwiwa ya kwato.

Kakakin ’Yan sandan ya ce sakamakon hadin kan da jama’a suke bayarwa wajen mika bindigogin Sufeto Janar din ya kara wa’adin mika bindigogin zuwa 30 ga Afrilun nan domin ba wadanda ba su mika nasu ba, damar su mika.

Moshoodya bayyana cewa Jihar Abiya ce aka fi kwatowa ko mika bindigogin inda aka kwato bindigogi 1,380, sai Legas ta biyo bay da bindigogi 200 nau’o’i daban-daban.

Sauran su ne, Katsina, 198 sai Ribas, 140, sai Birnin Tarayya, 78 sai Kaduna, 70 sai Kogi, 57 sai Borno, 32 sai Taraba, 56 sai Benuwai, 46 sai Nasarawa, 36 sai Adamawa, 14 da kuma Delta, 12.

Kwamitin cika aikin na hedkwata ya ce ya kwato bindigogi 435 da suka hada da AK47 guda 114 da fistol kirar Ingila guda 17 da bindiga kirar gida guda 27 da kuma barel guda 28. Sauran nau’o’in bindigogin da aka kwato sun hada da SMG guda 8 da Mark 1b 8 da fistol kirar gida 8 da harba-ka-ruga guda 38 da kuma ribalbal 28. 

Kakakin ’Yan sandan ya ce ’yan sanda sun kaddamar da raba jama’a da bindigogin ne domin a kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, inda ya ce an samu raguwar miyagun ayyuka da suka hada da fashi da satar mutane da shanu tunda aka fara shirin.  

Ya ce, “Sufeto Janar ya yi matukar jin dadi kan yawan mutanen da suka amsa kira suna mika bindigogin, wannan ne ya sa ya kara wa’adin zuwa karshen wannan wata.” Bayan karewar wa’adin, ’yan sanda za su kama duk wanda aka samu ya mallaki haramtattun bindigogi tare da gurfanar da shi a gaban kotu; ba za mu kama ko tsare duk wanda ya zo ya mika irin wadannan bindigogi da kansa ba.”

Kakakin ya ce za a mika bindigogin da aka kwato ga sashin adana makamai na ’yan sanda don adanawa yadda ya kamata da gudanar da bincike, “don gano ko an yi amfani da makaman wajen aikata miyagun ayyuka a baya,” inji shi.

Daga Kano, wakiliyarmu ta ce Rundunar ’Yan sandan Jihar ta karbo bindigogi kirar AK 47 guda 27 da wata kirar gida. Kuma akwai wadanda suka sallama nasu ga rundunar bisa radin kansu da suka hada da manyan bindigogi guda 4 da kirar refu 2 da barel 4 da fistol 23 sai kirar G3 Rifle guda 1 da Magnum Bow (ta Amurka) 1, sai abubuwa masu fashewa 10 da makunsan harsasai 17 da sauransu.

Kakakin Rundunar, SP Magaji Musa Majiya ya fadi a wata sanarwa cewa bayan karewar wa’adin duk wanda rundunar ta kama da bindiga zai fuskanci hukunci.