…’Yan sanda sun kwato shanu 200 daga barayi

Rundunar ’yan sandan Abuja ta samu nasarar kwato shanu 201 daga hannun wasu da ake zargin barayin shanu ne bayan ta kai farmaki a maboyarsu da ke dajin Kawu a karamar Hukumar Bwari ta yankin Birnin Tarayya, Abuja. Lamarin wanda ya faru a ranar Talatar makon jiya ya biyo bayan kwace shanu ne daga masu […]

…’Yan sanda sun kwato shanu 200 daga barayi
…’Yan sanda sun kwato shanu 200 daga barayi

Rundunar ’yan sandan Abuja ta samu nasarar kwato shanu 201 daga hannun wasu da ake zargin barayin shanu ne bayan ta kai farmaki a maboyarsu da ke dajin Kawu a karamar Hukumar Bwari ta yankin Birnin Tarayya, Abuja. Lamarin wanda ya faru a ranar Talatar makon jiya ya biyo bayan kwace shanu ne daga masu kiwonsu a ranar Lahadin makon jiya a kauyen Baran-Gwani da ke kusa da Bwari, kamar yadda daya daga cikin masu shanun ya shaida wa Aminiya.

Mai kiwon shanun mai suna Haruna Ibrahim da yanzu haka ke jinya a asibitin garin Kubwa sakamakon harbinsa a kafa da barayin suka yi, ya ce da farko sun yi kokarin bin barayin da nufin gano maboyarsu a daren da suka kai harin, amma sai suka sauya shawara bayan an harbe shi a kusa da kauyen Zuma da ke kusa da Bwari, lokacin da wasu daga cikin barayin suka labe da nufin auka wa masu bin su, yayin da sauran suka kora shanun.
Da aka tuntubi kakakin ’yan sandan Abuja, ASP Anjuguri Manzah ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an mika shanun ga masu su. Kuma sun samu nasarar fatattakar barayin daga maboyarsu, ya ce wasu daga cikin barayin sun samu raunin bindiga a yayin musayar wutar.