‘Yan sanda sun mamaye Hedkwatar PDP
Jami’an ‘yan sanda sun mamaye Hedkwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, bayan jam’iyyar ta fada rikicin shugabanci. Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargadi ‘yan PDP da su guji tayar da hankali ko kuma ta sanya kafar wando daya da su. Kakakin Rundunar ‘yan sanda, Olobisi Kolawole, ta aikewa kafafen watsa labarai wata sanarwa, inda a […]

Jami’an ‘yan sanda sun mamaye Hedkwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, bayan jam’iyyar ta fada rikicin shugabanci.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargadi ‘yan PDP da su guji tayar da hankali ko kuma ta sanya kafar wando daya da su.
Kakakin Rundunar ‘yan sanda, Olobisi Kolawole, ta aikewa kafafen watsa labarai wata sanarwa, inda a cikinta ta ce rundunar ta samu bayanan sirri da ke nuna cewa shugabanni da mambobin bangarorin jam’iyyar suna wani shiri na tayar da hankali ta hanyar amfani da ‘yan daba a Abuja yau Litinin. “Wannan ya sa Babban Sifeton ‘Yan Sanda, Solomon Arase, ya bayar da umarni a girke dakarunsa a hedkwatar domin dakile duk wani yunkurin tada zaune tsaye,” inji sanarwar.
A ranar Asabar ne jam’iyyar ta fada sabon rikici sakamakon cire shugabanta na riko, Sanata Ali Modu Sheriff da kuma maye gurbisa da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi. Sai dai Sherriff ya ce ba zai sauka ba. Har ila yau, akwai wani bangare na jam’iyyar da yake ikirarin cewa Sanata Ibrahim Mantu ne zai gaji Sheriff. Wannan ya sa a yanzu jam’iyyar ta rabu ne zuwa gida uku.