’Yan sanda sun mayar da N3.9m ga iyalan wanda ya rasu a hatsarin mota
’Yan sandan da ke aiki a yankin Soba a Jihar Kaduna sun mayar da Naira miliyan 3 da dubu 991 da 650 ga iyalan wani magidanci da hatsarin mota ya yi sanadiyar ajalinsa, Mustapha Sanusi. Jagoran rundunar ’yan sanda na yankin, Sufurtanda Pam Daniel Moses da ya ba da tabbaci kan samun wannan kudi a […]
’Yan sandan da ke aiki a yankin Soba a Jihar Kaduna sun mayar da Naira miliyan 3 da dubu 991 da 650 ga iyalan wani magidanci da hatsarin mota ya yi sanadiyar ajalinsa, Mustapha Sanusi.
Jagoran rundunar ’yan sanda na yankin, Sufurtanda Pam Daniel Moses da ya ba da tabbaci kan samun wannan kudi a tare da mamacin, ya ce hadarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 11 na safe a Unguwar Dan Isa da ke hanyar Pambeguwa zuwa Zariya.
Babban jami’in ya ce marigayi Mustapha Sunusi da ke cikin mota kirar Fijo 206 ya yo kokarin kauce wa rami ne sai ya bugi wata mota da ke kan hanyar zuwa Zariya, inda ya rasu nan take yayin da wadansu fasinjoji suka samu raunuka.
- Najeriya ta rasa kwararren matukin jirgin ruwa a hadarin mota
- Jadawalin Gasar Firimiyar Ingila na Makon farko
Ya ce bayan hadarin ne aka kira su, suka je sannan suka samu wani mutumin kirki kuma dan kasa na gari da ya dauki kudin ya rike har suka zo suka karba.
Ya ce bayan sun kai wadanda suka samu raunuka asibiti, sai suka kirga kudin a gaban mutane suka samu Naira miliyan 3 da dubu 991 da 650.
Shi ne suka mika kudin ga iyalan mamacin a ranar Talatar da gabata da motarsa ga amininsa Alhaji Kabiru Garkuwan Soba kuma dukkan bangarorin biyu sun yi wa juna afuwa.
Iyalan marigayin sun yaba wa mutumin da ya fara dauko kudin da ’yan sanda da suka nuna halin kwarai.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ASP Aliyu Jalige kan lamarin, ya ce zai kira amma har lokacin hada rahoton bai kira ba.