’Yan sanda sun sa dokar hana yawon dare a Gombe

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanar a ranar Alhamis cewa dokar za ta fara aiki ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025.

’Yan sanda sun sa dokar hana yawon dare a Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta haramta yawon dare, ta hanyar takaita zirga-zirga daga kare 12 na dare zuwa 5 na asubahi.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanar a ranar Alhamis cewa dokar za ta fara aiki ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025.

Ya bayyana cewa an kafa dokar takaita zirga-zirgar ne bayan samun rahotannin barazanar tsaro.

Sanarwar ta ce, “takaita zirga-zirgar na da nasaba da karuwar barazanar tsaro da ke fuskantar al’ummar Gombe,” kuma a shirye rundunar take ta shawo kansu.

DSP Buhari ya kara da cewa rundunar za ta kara ba da muhimmanci ga tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma domin jihar Gombe ta kasance cikin aminci.

Ya bukaci jama’a su ba da hadin kai, yana mai kira ga iyaye da su gargadi ’ya’yansu su guji saba dokar domin duk mai kunnen kashin da aka kama zai yaba wa aya zaki.