’Yan sanda sun saci fetur a sabon filin jirgin saman Bauchi
Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta fara bincike kan zargin cewa “An kama wasu ’yan sanda uku kan sacewa da sayar da fetur din gwamnati a sabon filin jirgin sama na kasa da kasa da ake ginawa a Jihar. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar ASP Hassan Muhammed Auyo ya tabbatar da lamarin ga manema labarai […]

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta fara bincike kan zargin cewa “An kama wasu ’yan sanda uku kan sacewa da sayar da fetur din gwamnati a sabon filin jirgin sama na kasa da kasa da ake ginawa a Jihar. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar ASP Hassan Muhammed Auyo ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a Bauchi a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce “An kama ’yan sandan da ake zargi, kuma ana yi musu tambayoyi a sashin binciken manyan laifuffuka (CID) kuma Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da laifi a karshen binciken kamar adda dokar aikin dan sanda da dokokin kasa suka tanada.”
Wani babban jami’in tsaro ya shaida wa manema labarai cewa, “Jami’an ’yan sandan da ake zargin sun saci fetur din gwamnati sun hada da wani sufeo da kofur da saje, kuma mun kwao jarkoki da dama da mota kirar Starlet da suke amfani da ita wajen daukar man zuwa kasuwa.”
Ya ce a karshen bincike za a yyi musu korar kare daga aikin dan sanda a gurfanar da su a kotu in aka same su da laifi, saboda muna aiki wurjanjan domin raba aikin dan sanda da baragurbi, domin aikinsu abin kunya ne, kuma baragurbi ne a cikin aikin.”