’Yan sanda sun sha alwashin tabbatar da tsaro a yayin Kirsimeti

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta haramta amfani da kayayyakin fashewa na nok-awut da shirya bukuwanan da akan kwana ana yi a kan manyan tituna a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara. A cewar Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sandan shiyya ta 2 da ke Onikan Legas, CSP Adebowale Lawal; rundunar ta dauki matakin ne […]

’Yan sanda sun sha alwashin tabbatar da tsaro a yayin Kirsimeti
’Yan sanda sun sha alwashin tabbatar da tsaro a yayin Kirsimeti

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta haramta amfani da kayayyakin fashewa na nok-awut da shirya bukuwanan da akan kwana ana yi a kan manyan tituna a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

A cewar Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sandan shiyya ta 2 da ke Onikan Legas, CSP Adebowale Lawal; rundunar ta dauki matakin ne domin kare dukiya da rayukan al’umma a lokacin bukukuwan na Kirsimeti da sabuwar shekara. “La’akari da umarnin da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Solomon Arase ya bayar na hana amfani da nok-awut da sauran abubuwa masu fashewa da bukukuwan kalankuwa da ake kwana ne ya sanya su nanata  umarnin domin hana batagari fakewa da hakan wajen cutar da jama’a lokacin bukukuwan.
Ya cewa a lokacin ire-iren wadannan bukukuwa ne ’yan kungiyoyi asiri masu gaba da juna kan kai wa junansu farmaki a garuruwan Legas da Ogun, wanda rundunar ba za ta lamince mawa ba a bana, “Domin haka duk wanda ke son gudanar da irin wannan bikin sai ya nemi izini daga shugaban ’yan sandan da ke yankin,” inji shi. Ya ce tuni jami’ansu ke zarya a kasuwani domin ganin ba a sayar da nok-awut a jihohin Legas da Ogun ba.
A karshe, ya yaba wa kafafen watsa labarai bisa gagarumar gudunmawar da suke ba rundunar wajen tabbatar da tsaro.