’Yan sanda sun shiga karkashin mota don ceto ’yar kyanwa da ta makale
Rundunar ’Yan sandan New York a Amurka ta nuna wani hoton jarumtar da jami’anta hudu suka nuna wajen ceto ran wata ’yar kyanwa da ta makale a kasar injin wata mota. ’Yan sandan na shiyya ta 32 a garin Harlem, su bakwai ne suka samu rahoton ’yar kyanwar ta makale nan da nan suka hada […]
Rundunar ’Yan sandan New York a Amurka ta nuna wani hoton jarumtar da jami’anta hudu suka nuna wajen ceto ran wata ’yar kyanwa da ta makale a kasar injin wata mota.
’Yan sandan na shiyya ta 32 a garin Harlem, su bakwai ne suka samu rahoton ’yar kyanwar ta makale nan da nan suka hada gwiwa da rundunar jami`an tsaro na musamman zuwa yankin da motar take.
’Yan sandan yankin sun sanar da hakan ne a shafinsu na Tiwita tare da hotunan ’yan sandan lokacin da suke kokarin ceto ’yar kyanwar a karkashin motar don ceto rayuwarta kamar sauran dabbobi saboda zaman ’yar kyanwar a cikin injin motar na iya sanadiyyar rasa ranta.
“Zaman kyanwar a injin motar bai dace ba,” in ji ’yan sandan.