’Yan sanda sun soke duk taron kamfe a Kano saboda rikici

Matakin ya biyo bayan harin da aka kaiwa mabiyan Kwankwaso ranar Alhamis

’Yan sanda sun soke duk taron kamfe a Kano saboda rikici

‘Yan Sanda a bakin aiki

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da soke dukkanin tarukan yakin neman zaben da ake gudanarwa a a jihar ranar Alhamis.

Jam’iyyar APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa a jihar ta NNPP sun shirya gudanar da kamfe din na su na karshe ne ranar Alhamis din, gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisun Tarayya da za a gudanar ranar Asabar.

To sai dai rikicin magoya baya ya sanya rundunar ’yan sandan jihar gayyato shugabannin jam’iyuun biyu, da kuma cikon ta uku wato PDP taron gaggawa, inda suka shawarce su su janye kamfe din.

Wata majiya ta ce jagororin APC da NNPP sun yi watsi da shawarar, amma rundunar ta ce ba gudu ba ja da baya kan hanin.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar dauke mai dauke da sa hannun mataimakin kwamishinan ’yan sandan jihar DCP Muhammad ya ce rundunar ta shawarci dukkanin jam’iyyun da su dakatar da kamfe din na Shugaban Kasa da ’yan majalisun taraya zuwa wani lokaci bayan ranar 25 ga watan Fabrairu.

“Duba da halin da tsaro ya shiga a jihar da kasa baki daya, Kwamishinan ’yan sanda ya kira wakilan jam’iyyun uku taron gaggawa don lalubo mafita.

“Mun shawarce su su janye tarukan kamfe na shugaban kasa da ’yan majalisun taryya zuwa bayan zaben ranar Asabar”, in ji shi.

A hannu guda shugabannin APC sun shaida wa wakilinmu cewa jam’iyyar za ta ci gaba da taron ta na Kulob Rod, yayin da NNPP za ta yi na ta a Kwanar Dangora, daga nan magoya baya su wuce gidan dan takarar shugaban kasarsu Rabiu Kwankwaso da ke Miller Road.