‘Yan sanda sun tabbatar da yin garkuwa da manomi a Gombe
Hukumar ‘yan sandan jihar Gombe, sun tabbatar da yin garkuwa da wani manomi dan shekara 59 mai suna Shugaba Garba a unguwar Tudu-Koya da ke karamar hukumar Billiri a jihar. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Mohammed Mukaddas, ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin a Gombe. Mukaddas ya ce, a yanzu haka hukumar tsaron na […]
Hukumar ‘yan sandan jihar Gombe, sun tabbatar da yin garkuwa da wani manomi dan shekara 59 mai suna Shugaba Garba a unguwar Tudu-Koya da ke karamar hukumar Billiri a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Mohammed Mukaddas, ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin a Gombe.
Mukaddas ya ce, a yanzu haka hukumar tsaron na binciken lamarin lokacin da ya ziyarci yankin.