’Yan sanda sun budewa mabiya shi’a wuta a Abuja
Rahotanni a babban birnin tarayya Abuja na cewa ‘yan sanda sun bude wuta a kan mabiya mazhabar Shi’a masu zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky yau Litinin. Rahotan na bayyana cewa, an harbi wasu daga cikin ‘yan shi’an lokacin da ‘yan sandan suka dinga harba barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar a wajen […]
Rahotanni a babban birnin tarayya Abuja na cewa ‘yan sanda sun bude wuta a kan mabiya mazhabar Shi’a masu zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky yau Litinin.
Rahotan na bayyana cewa, an harbi wasu daga cikin ‘yan shi’an lokacin da ‘yan sandan suka dinga harba barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar a wajen da suka taru kusa da babbar Sakatariyar gwamnati.
Gidan talbijin na ChannelsTV ya ce an harbi daya daga cikin ma’aikatansu a ciki a lokacin yamutsin.
Wasu daga cikin ‘yan shi’an sun ce, ‘yan sanda ne suka bude musu wuta alhali su ba su da makamai lokacin da suke zanga-zangar.