’Yan sanda sun tarwatsa taron kaddamar da takarar Tata
’Yan sanda a Jihar Katsina sun tarwatsa taron kaddamar da dan siyasar nan da ya yi suna wajen taimakon marasa karfi, Alhaji Umar Abdullahi Tsauri da aka fi sani da Tata a matsayin mai son tsayawa takarar Gwamna a Jihar Katsina. Bayanai sun ce Tata ya sayi takardar nuna sha’awarb tsayawa takarr Gwamna a hedkwatar […]
’Yan sanda a Jihar Katsina sun tarwatsa taron kaddamar da dan siyasar nan da ya yi suna wajen taimakon marasa karfi, Alhaji Umar Abdullahi Tsauri da aka fi sani da Tata a matsayin mai son tsayawa takarar Gwamna a Jihar Katsina.
Bayanai sun ce Tata ya sayi takardar nuna sha’awarb tsayawa takarr Gwamna a hedkwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja, kuma ya shirya taron a ranar Asabar a filin Polo don kaddamar da kansa a matsayin daya daga cikin masu son tsayawa takarar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina Mataimakin Sufurtanda Aminu Sadik ya ce, rundunar ta hana taron ne don ya saba wa dokar hukumar zabe ta kasa (INEC) na hana kamfe har sai wata uku kafin ranar zabe, wanda ya dace da ranar 18 ga Nuwamba mai zuwa.
Ya ce, sun shaida wa Tata ya yi hakuri da yin kamfe, amma a cewarsa Tata bai ji ba hakan ya sa rundunar ta dauki matakin hana taron.
DSP Aminu ya ce, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Muhammad D. Hurdi ya yi taro da jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki a harkokin zabe ciki har da dokokin da aka shimfida a kan zaben a kwanakin baya.
Aminiya ta ce alamun hana taro sun bayyana tun dare inda ’yan sandan suka je filin polo suka kori jama’ar da ke wurin ciki har da masu gadin kujeru da kayan da aka tanada don taron, inda aka zargi ’yan sandan da sanya wa kayan wuta kuma haka ya janyo konewar babbar rumfar da sarki da manyan mutane ke zama a lokacin wasan polo ko wasu manyan tarurruka a filin, kamar yadda shaidun da suka nemi a sakaya sunayensu suka ce.
’Yan sandan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa magoya bayan Tata da suka tarbe shi a filin jirgi sama na Umaru ’Yar’aduwa da ke Katsina.
Wani mazaunin Katsina mai suna Mamman ya nuna takaici a kan wannan mataki. Ya ce, Tata na da ’yanci kamar kowa, kuma in bai zo Katsina ya bayyana kudurinsa ba ina ake so ya je?
“Ba fa yawon kamfen ya fito ba, ya zo ne don ya shaida wa al’ummar Jihar Katsina zai shiga neman tsayawa takara, sai a hana shi? Buhari da Atiku duk sun yi haka, ga Jonathan ya ce zai bayyana kansa a ranar 11 ga Nuwamba. Irin wannan matakan ke kara wa Jam’iyyar PDP bakin jini a Jihar Katsina,” inji wani da ya nemi a boye sunansa.
Sai dai wani da Aminiya ta tuntuba ya ce, matakin da aka dauka ya yi don nuna wa saura cewa, babu ruwan doka da wane.
Ba a yi taron ba kamar yadda aka shirya illa an yi jerin gwano zuwa wasu wurare a cikin gari inda a karshe bisa titi Tata ya ba magoya bayansa hakuri ya juya ya shiga jirgi ya koma inda ya fito.