`Yan sanda sun tsare malamin da yake lalata da almajiransa
Hukumar ‘yan sandan jihar Sakkwato sun tsare wani malamin makarantar almajirai mai suna Malam Murtala Mode, da ke yankin Arkillan Magaji a jihar. Ana zargin malamin ne da yin lalata da almajiransa su shida. Bayan tsare malamin ya bayyana cewa, ya aikata hakan a bisa tsautsayi da kuma saboda kudi. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sakkwato […]
Hukumar ‘yan sandan jihar Sakkwato sun tsare wani malamin makarantar almajirai mai suna Malam Murtala Mode, da ke yankin Arkillan Magaji a jihar. Ana zargin malamin ne da yin lalata da almajiransa su shida.
Bayan tsare malamin ya bayyana cewa, ya aikata hakan a bisa tsautsayi da kuma saboda kudi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sakkwato Ibrahim Kaoje, ya ce a ranar 22 ga watan Mayu 2019 wani lauya Barista Hamza Liman, ya karar malamin ofishin ‘yan sanda na Arkilla. Malamin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.