’Yan sanda sun tsinci gawar budurwa a Jihar Nasarawa

’Yan sanda da ke tsintiri da daddare a yankin Unguwar Nunku da ke garin Lafiya a Jihar Nasarawa sun tsinci gawar wata budurwa mai kimanin shekara 19 mai suna A’isha Musa Laminu da aka fi sani da Anty, lamarin da ya jefa mutanen unguwar a cikin jimami. Da wakilinmu ya ziyarci gidan iyayen marigayiyar wani […]

’Yan sanda sun tsinci gawar budurwa a Jihar Nasarawa
’Yan sanda sun tsinci gawar budurwa a Jihar Nasarawa

’Yan sanda da ke tsintiri da daddare a yankin Unguwar Nunku da ke garin Lafiya a Jihar Nasarawa sun tsinci gawar wata budurwa mai kimanin shekara 19 mai suna A’isha Musa Laminu da aka fi sani da Anty, lamarin da ya jefa mutanen unguwar a cikin jimami.
Da wakilinmu ya ziyarci gidan iyayen marigayiyar wani mai suna Aminu Laminu wanda ya yi magana a madadin iyayen A’isha ya ce a ranar Litinin ne sai suka samu labari cewa wasu ’yan sanda da ke tsintiri a yankin sun samu gawar kanwarsu Aisha cikin dare kuma sun kai Asibitin kwararru na dalhatu Araf da ke Lafiya. Ya ce sun aika aka bincika a gidan wani wan mahaifin A’isha mai suna Alhaji A.D. Bello inda ya ce ta bar gidansa kwana uku da suka gabata cewa za ta halarci wani bikin aure a gidan mahaifinta kuma tun daga lokaci suna tunani can take.
Daga nan a cewar Aminu sai suka tafi asibitin inda suka bincika aka kuma tabbatar musu cewa lallai an kawo gawar kanwarsu A’isha asibitin amma mahukuntan asibitin sun ki amincewa su dauki gawar inda suka gaya musu cewa sai sun je sun nemi izinin ’yan sanda da suka kawo gawar kafin a ba su.
Ya ce da suka dawo ofishin ’yan sandan suka bayyana musu sai suka ba da izini suka je suka dauki gawar suka binne.
Ya bayyana A’isha da mai ladabi da biyayya marar fada, a koyaushe za ka ganta cikin fara’a da mutunci da kowa. Ya yi mamaki yadda wasu marasa imani suka kashe ta inda ya yi addu’ar Allah Ya jikanta.
Ita dai A’isha Musa Laminu, kafin ta gamu da ajalinta a hannun miyagun mutanen tana zaman goyo ne a gidan Alhaji Bello, kuma da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakinsa game da lamarin, ya ce ba za su iya cewa komai ba a halin yanzu saboda suna cike da jimamin lamarin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar ASP Norman Usman ya bayyana wa wakilinmu a lokacin da ya tuntube shi cewa wasu jami’ansu ne da suke tsintiri a hanyar Unguwar Nungu zuwa Kwandare suka ga gawar marigayiyar da misalin karfe 2:00 na dare a gindin wata bishiya.
Ya ce tuni rundunar ta soma binceke a kan lamarin don ganowa da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi