Tsaro: ’Yan sanda sun tura motocin sulke 13 zuwa Kebbi

Ya ƙara da cewa wannan ƙarfafawa na nufin inganta tasirin ayyukan rundunar, faɗaɗa sintiri, da kuma tallafawa gaggawar amsa matsalolin tsaro a faɗin jihar.

Tsaro: ’Yan sanda sun tura motocin sulke 13 zuwa Kebbi

’yan Sanda

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kebbi ta karɓi motocin sulke guda 13, da sauran motocin aiki daga Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kebbi, Bello M. Sani, ya mika motocin ga Gwamna Nasir Idris a Fadar Gwamnatin Jihar a ranar Litinin.

Ya ce: “Sufeto-Janar ya ga dacewar ƙarfafa ƙoƙarinku wajen shawo kan matsalolin tsaro a jihar ta hanyar samar da ƙarin motocin sulke da sauran motocin aiki domin ƙara nasarorin da aka samu.”

Ya ƙara da cewa wannan ƙarfafawa na nufin inganta tasirin ayyukan rundunar, faɗaɗa sintiri, da kuma tallafawa gaggawar amsa matsalolin tsaro a faɗin jihar.

Kwamishinan ya jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar wa jama’a cewa za a yi amfani da sabbin kayan aikin cikin tsari domin ƙarfafa tsaro a dukkan sassan jihar.

Gwamna Idris ya yaba wa Sufeto Janar na ’Yan Sanda da Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi bisa ƙoƙarinsu na ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin haɗin gwiwa da ‘Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro domin shawo kan ayyukan laifi a jihar.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki