‘Yan sanda sun warware shirin garkuwa da Sarkin Sanga a Kaduna
Tuni aka baza jami’an tsaro a dazuzzukan da ke kusa da Sanga domin neman matar.
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar daƙile harin da wasu ’yan bindiga suka kai wa Sarkin Masarautar Ninzo da ke Ƙaramar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna.
Bayanai sun ce basaraken ya tsallake rijiya da baya yayin da ’yan bindigar suka yi azamar garkuwa da shi a daren ranar Laraba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa har yanzu ba a san inda matar sarkin take ba.
Mansir ya ce tuni aka baza jami’an tsaro a dazuzzukan da ke kusa da Sanga domin nemo matar.
Ƙungiyar ci gaban Ninzo, a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabanta da sakatarenta, Farfesa Moses Audi da Silas Anche, sun yi Allah wadai da wannan lamari wanda ya kai ga ɓacewar matar sarkinsu na gargajiya.
Sai dai sanarwar ta yi kira da a kwantar da hankula domin bai wa gwamnati damar gudanar da ayyukanta.