’Yan sanda sun warware takaddama a kan jana’izar wata budurwa
Rasuwar wata budurwa mai shekara 25 mai suna biola Umar a Layin Ja’o’ji a Unguwar Gyadi- Gyadi, Kano ta jawo takaddama a tsakanin iyayenta da mutanen unguwa bayan da suka nemi su yi mata jana’iza ta Kirista mutanen unguwar kuma suka ce za su yi mata jana’iza ta Musulunci, kafin ’yan sanda su warware takaddamar. […]

Rasuwar wata budurwa mai shekara 25 mai suna biola Umar a Layin Ja’o’ji a Unguwar Gyadi- Gyadi, Kano ta jawo takaddama a tsakanin iyayenta da mutanen unguwa bayan da suka nemi su yi mata jana’iza ta Kirista mutanen unguwar kuma suka ce za su yi mata jana’iza ta Musulunci, kafin ’yan sanda su warware takaddamar.
Jayayyar ta fara da kirawo jami’an Hisbah daga nan aka tafi ofishin ’yan sanda na ’Yar Akwa da gawar marigayiya biola da makwabta da yayarta Salamatu, wata matar aure Musulma, inda suka gamsar da ’yan sanda cewa biola ta rasu tana Musulma.
Jami’in Hisbah na Tarauni Malam Rabilu Sani ya shaida wa Aminiya cewa, mahaifiyar biola da wakilin mahaifinta duk sun je wurin ’yan sandan kuma sun gamsu da shaidar da jama’a suka bayar cewa Musulma ce.
Wani makwabcin su biola, Malam Aliyu Mukhtar Saleh ya ce a wajensu ta musulunta, “Na ganta ta yi Sallah fiye da sau dari, kuma na gan tana azumi sau da yawa, har azumin Litinin da Alhamis take yi,” inji shi. Ya ce lokacin da iyayen biola suka fito da ita daga gida zuwa asibiti wasu daga cikin masu raka su sun ji tana furta Kalmar Shahada, kafin ta cika.
Mahaifin biola, Mista Fidelis Umar da Aminiya ta tarar a kusa da gawarta yana jawabi, ya fada wa wakilinmu cewa abin da ya sa suka nemi yi mata jana’iza shi ne don “ban taba sanin ta musulunta ba.” Ya ce amma daga baya ya gamsu, tunda shaidu sun tabbatar ciki har da yayarta wadda Musulma ce. Ya ce “na yafe mata, tun da ta riga ta rasu.”
Mahaifiyar biola, Maslina Umar ta nuna damuwarta kan rashin ’yarta, sannan ta ce ta gamsu cewa ta musulunta. Ta ce “Na bar komai a wajen Ubangiji kuma ba ni da kaico a kan wannan rashin.” Ta bayyana marigayiya biola da yarinya mai ladabi da biyayya da haba-haba da jama’a.
Mai unguwar ’Yar Akwa, Malam danladi Musa ya ce a gabansa aka yi komai kuma ya ji dadin yadda aka bi hanyar hukuma da lumana aka warware batun.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da faruwar lamarin.