‘Yan sanda sun yi awan gaba da wakilin Daily Trust

‘Yan sanda sun yi awan gaba da wakilin Jaridar Daily Trust da Aminiya na Majalisar Wakilai na tarayya Musa Abdullahi Krishi a lokacin da yake gudanar da aikinsa a majalisar. Har yanzu babu labarin inda suka kai shi, sannan ana dari darin cewa yana cikin wani hali domin duk kokarin da aka yi na samunsa […]

‘Yan sanda sun yi awan gaba da wakilin Daily Trust

‘Yan sanda sun yi awan gaba da wakilin Jaridar Daily Trust da Aminiya na Majalisar Wakilai na tarayya Musa Abdullahi Krishi a lokacin da yake gudanar da aikinsa a majalisar.

Har yanzu babu labarin inda suka kai shi, sannan ana dari darin cewa yana cikin wani hali domin duk kokarin da aka yi na samunsa a waya abin ya ci tura domin wayoyinsa duk suna kashe.

Har yanzu ‘yan sanda basu sanar da kamfanin jaridar Daily Trust ko me ya sa suka yi awan gaba da wakilin ba.