‘Yan sanda sun yi gargadi akan sayen wayar sadarwa

Shugaban ofishin ‘yan sandan Ilaro SP. Oni Waheed, ya shawarci jama’a akan sayen wayar sadarwa daga hannun bakin da ba a sani ba, don kauce wa sabawa doka. Waheed ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da Kamfanin dillancin labarai NAN a yau Alhamis a garin Ota jihar Ogun. Ya kara da cewa, a maimakon jama’a […]

‘Yan sanda sun yi gargadi akan sayen wayar sadarwa

Shugaban ofishin ‘yan sandan Ilaro SP. Oni Waheed, ya shawarci jama’a akan sayen wayar sadarwa daga hannun bakin da ba a sani ba, don kauce wa sabawa doka.

Waheed ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da Kamfanin dillancin labarai NAN a yau Alhamis a garin Ota jihar Ogun.

Ya kara da cewa, a maimakon jama’a su rika sayen waya a hannun wadanda basu sani ba, ya dace su rika saya a wajen da kowa yake saya don kauce wa fadawa tarkon ‘yan sandan.