’Yan sanda sun yi wa sakatariyar APC ta kasa kawanya
Jami’an dai sun isa sakatariyar ne a kan motoci kirar Hilux, sannan suka mamaye ta.
Tarin jami’an ’yan sanda dauke da manyan makamai a ranar Laraba sun yi wa sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja kawanya.
Jami’an dai sun isa sakatariyar ne a kan motoci kirar Hilux, sannan suka mamaye muhimman wurare na gininta.
- Motar giya ta fadi a kusa da ofishin Hisbah a Kano
- Bayan gargadin Buhari ’yan bindiga sun kashe mutum 15 a Sakkwato
Aminiya ta gano ta bakin wasu majiyoyi daga ’yan sanda cewa an dauki matakin ne bayan wasu bayanai sun nuna akwai masu zanga-zanga da ke kokarin taruwa a ginin.
Rahotanni dai sun ce wasu fusatattun ’ya’yan jam’iyyar sun shirya yin zanga-zangar kin amincewa da shugabancin riko na jami’yyar karkashin Gwamna Mai Mala Buni.
Da yake tsokaci a kan lamarin, Sakataren jam’iyyar na riko, Sanata John Akpanudoedehe, ya shaida wa ’yan jarida cewa jami’an tsaro sun yi wa sakatariyar kawanya ne bayan bayanan sirrin da suka samu.
“Babu abin da yake faruwa. Suna zuwa nan a duka lokacin da muke bukatar tsaro a sakatariyarmu.
“Wannan abu ne da aka saba gani. ’Yan sanda na aiki tare da Ministan Abuja da Babban Sufeton ’Yan sanda a duk lokacin da ake da wani rahoto.
“Ba iya nan kwadai ba, idan kana tahowa daga hanyar filin jirgin sama zaka ga wasu, mune ke da alhakin kare rayukan mutanen da ke aiki a nan.
“Muna aiki ne da rahotannin tsaro, amma ina mai tabbatar maka babu wani abin fargaba a ciki,” inji shi.