‘Yan sanda sun zafafa kame bayan kisan Abuja
Bayan farmakin da jami’an tsaro suka kai wa wani gida da ba a kammala ba a unguwar Apo da ke Abuja har mutum takwas suka rasa ransu, rundunar ’yan sandan Abuja ta kaddamar da samame a wadansu gine-ginen da ba a kammala ba da mutane ke zaune a yankunan birnin tarayya, inda wadanda al’amarin ya […]

Bayan farmakin da jami’an tsaro suka kai wa wani gida da ba a kammala ba a unguwar Apo da ke Abuja har mutum takwas suka rasa ransu, rundunar ’yan sandan Abuja ta kaddamar da samame a wadansu gine-ginen da ba a kammala ba da mutane ke zaune a yankunan birnin tarayya, inda wadanda al’amarin ya rutsa da su suka samu kansu cikin mawuyacin hali.
daya daga cikin wadannan wurare shi ne wani rukunin gidaje da ake kira NEPA kuarters da ke kan hanyar yankin Gwarinpa daga unguwar Mabushi da ke Abuja. Wani da ya ga lokacin da jami’an ’yan sandan a wajen, mai suna Muhammadu Bello Alkali, da ke sana’ar tuka tasi a unguwar Mabushi, ya bayyana cewa, “da misalin karfe takwas na dare motocin ’yan sanda kirar Hilus, wadanda ba za su gaza 12 ba da kuma doguwar mota kirar Tata da kuma motoci masu sulken yaki guda biyu suka yada zango a daura da babban ofishin ’yan sanda na Mabushi. Wadansu motocin a lokacin da suka iso mu suka tambaya muka nuna musu ofishin ‘yan sandan. Haka dai suka yi ta zuwa har wajen karfe goma sannan suka bar wajen ba tare da sun kama kowa ba, sai dai mutane sun yi ta gudu, har wadansu sun ji rauni saboda tsoron ko za a kama su.’’
Da jami’an yan sandan suka isa rukunin gidajen NEPA kuarters, bayan sun taso daga Mabushi, mazauna wajen da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa, an kama mutane sama da 200. Mai unguwar yankin Malam Ashiru Sule da ya ce, “akwai kabilu daban-daban a yankin, amma dai Hausawa suka fi yawa, kuma kowa ka gani a nan da sana’arsa, in ban da yara kankana. Muna zaman lafiya, kuma da sanin jami’an tsaro da ke hulda da mu masu kaki da na farin kaya. A daren da aka kawo samamen da misalin karfe goma na dare, na bukaci jama’a da su guji yin guje-guje don kada a harbe su, inda na nuna musu gara a kama su.’’
Wani mai suna Ahmad Umar, da ke sana’ar sayar da kaya a shago, ya ce a lokacin da aka kawo samamen wadansu na wajen sana’a ko hira, wadansu kuma suna barci. A bangarenmu kadai an kama mutane wajen 120, da farko wadansu sun nuna turjiya, amma sai suka ce mana bincike kawai za su yi, sai dai bayan da muka bi su, babu wani bincike in banda kudi da suka nema daga wajenmu. Wadansu leburori ne ba su yi aikin komi ba a ranar da aka wuce da mu, kashegari sai suka karbi Naira dubu uku daga wajen wadansu, wadansu kuma Naira dubu biyu. Wadansu ko ba su da komai, sannan suka sake mu muka dawo.’Shi kuwa Aminu Muhammad wanda ke sana’ar tuka Keke NAPEP, kokawa ya yi da yanayin da aka kama su, ya ce, “mu wajen 150 aka wuce da mu ofishin ’yan sanda na ZONE 3, ba abinci ba ruwa, balle damar yin sallah, a tsawon zaman da muka yi a wajen, daga dare zuwa kashegari da yamma, wadansu daga su sai zani ko kamfe, kasancewar an kama su su a barci a makwancinsu ba tare da sun san abin da ke tafe ba. Sun yi mana tambayoyi a kan makaranta da muka yi ta allo da ta boko, da dai sauransu, kafin daga bisani suka sake mu.’’