’Yan sanda sun zargi sojoji da kashe jami’ansu uku da sake mai garkuwa da mutane a Taraba
Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta zargi wadansu sojoji da hallaka jami’anta uku tare da raunata wasdanu bayan da sojojin suka bude wa ’yan sandan wuta a Jihar Taraba. Lamarin ya faru ne a hanyar Ibi zuwa Jalingo, kamar yadda sanarwar da ’yan sandan suka fitar ta bayyana, inda ta ce ayarinta na kai daukin gaggawa […]
Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta zargi wadansu sojoji da hallaka jami’anta uku tare da raunata wasdanu bayan da sojojin suka bude wa ’yan sandan wuta a Jihar Taraba.
Lamarin ya faru ne a hanyar Ibi zuwa Jalingo, kamar yadda sanarwar da ’yan sandan suka fitar ta bayyana, inda ta ce ayarinta na kai daukin gaggawa ne Intelligence Response Team (IRT) sojojin suka yi wa barnar.
Sanarwar ta ce ayarin a karkashin jagorancin Mataimakin Sufurtanda Felid Adolije, ya je jihar ce don kama wani da ake kira Alhaji Hamisu da ake zargi da satar mutane ne.
Sanarwar ’yan sandan ta kara da cewa ’yan sandan sun kamo mutumin ne za su kai shi hedkwatarsu a Jalingo lokacin da sojojin suka bude musu wuta, duk da cikakkiyar shaidar da ke nuna cewa suna kan aikinsu ne.
A nasu bangaren, Kakakin Sojin Najerya Kanar Sagir Musa ya musanta zargin na ’yan sanda, inda ya ce sun yi ba-ta-kashi ne da masu satar mutane.
Kanar Sagir Musa ya ce sojojin sun yi tsammanin ’yan sandan tawaga ce ta masu satar mutane domin wadansu mutane daga yankin sun nemi a kai musu dauki saboda masu satar jama’a sun kai musu hari.
A dalilin haka ne suka “tsayar da mutanen da ke tafiya a wata motar Bas amma suka ki tsayawa, dalilin da ya sa suka bude musu wuta domin kubutar da mutanen da ake zargin an sace.” Kamar yadda BBC ya ruwaito.
“Sai daga baya ne daya daga cikin wadanda suka tsira ya shaida mana cewa su ’yan sanda ne daga Abuja, kuma an turo su ne domin gudanar da wani aiki na musamman kan masu satar mutane,” inji shi.
Sojojin sun ce ’yan sandan ba su sanar da su cewa za su gudanar da wannan aiki ba, kuma rundunar ’yan sandan Jihar Taraba ta ce ba ta san da zuwansu ba.
‘Yan sandan suna zargin mutumin, Alhaji Hamisu da kasancewa mai satar mutane, da suka dade suna nema saboda hannu a sace-sacen jama’a, ciki har da sace wani dan kasuwa mai harkar mai da aka yi kwanakin bayn a jihar ta Taraba.
Shugaban Rundunar ’Yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya bayar da umarnin a gudanar da binciken gaggawa kan lamarin, kamar yadda Kakakin Rundunar, Mista Frank Mba ya sanar.
Su ma sojoji ta bakin Kanar Sagir Musa sun ce suna kiran da a kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa a karkashin jagorancin ’yan sandan domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.